TAFIYA MABUDIN ILIMI!!!.
Alhamdulillahi Yanzu Haka ina acikin Garin Kano ta Dabo tunbin Giwa Ance Koda me Kazo anfika.
Babu Shakka Tafiya Mabudin ilimi ce na shiga Kano anfi a kirga Amma Wannan yafiyar kasancewar ta ta Daban Kuma ta Musamman nayi kokarin Yin Karatu kadan don samun Ilimi kamin Isa Kasa Mai Tsalki.
Kano akwai Arziki na ALUMMA Musamman Matasa Masu Harkar yi, Duk yadda kaga Matashi Dan Social Media Yana rubuta na Siyasa irin Namu zaka same shi Yana da Sana'a a Kano komai kankantar ta wadda Yake amfani da ita wajen Kare Mutumcin sa. Saidai yakan nemi Karin Jari don habaka kasuwancin NASA.
Haka muma anan Jahar Kebbi Yan Social Media dinmu mafi yawancin mu muna Sana'a nasani wasun mu Tailoli ne, Wasu Shaguna garesu suna saida kayan Masarufi, Wasu suna Gyaran Wuta, Wasu Kamar Ni muna saida Wayoyi da kayan Waya. Wasu Kuma saida Kati daidai Sauran su.
Kamar Ni Yahuza Zaki Gwandu sanin kowane Duk Wanda yasanni yasanni Ina Sana'ar Dinki da Farko kamin in Koma Sana'ar Saida Waya, Kayan waya da katin Waya da Layi inda hakan yabani dama nayi Aiki a Kamfanin MTN amatsayin (Sales Representative da Customer Care Representative) a Sashe biyu na Kamfanin MTN.
Da haka Nike kara Godiya ga Allah subhanahu wata'ala bisa Wannan Ni'ima da Yayi muna na kara muna Daga cikin Harkar mu ta Sana'ar waya da Kati na Samun Kari na Social Media aciki Sana'ar mu ta Waya.
Allah abin Godiya ya Allah ka qara haskaka muna Wannan Sana'a TAMU ka Kara inganta muna ita. Yanzu haka Kuma zaku iya Kirana da Sunan Dan Jarida Journalist kasancewar nasamu Takardar shedar Zama Haka, ko kuma ku Kira Dan Jarida na Zamani saboda Aikin Jaridar da Mukeyi a Kafafen Sada Zumunta na Zamani watau Social Media.
NAGODE NAGODE NAGODE
Naku Akoda yaushe.
Yahuza Zaki Gwandu
1. Managing Director
Annur Communication Limited.
Director General
2. Annur New Media Reporters Service Nigeria.
Friday 01 February 2019.
Comments
Post a Comment