www.annur.com.ngMATAKI NA GABA ( NEXT LEVEL ) MATASA SUN BAYYANA FARIN CIKIN SU BISA NASARAR DA JAMIYAR APC TASAMU NA LASHE ZABEN 2019 NA SHUGABAN KASA MUHAMMADU BUHARI DA "YAN MAJALISUN DATTAWA DA NA TARAYYA BAKI DAYA A JAHAR KEBBI.
Rahoton
Yahuza Zaki Gwandu
Daga Birnin Kebbi, Jahar Kebbi.
1. A Jiya Larba 27 February 2019 ne Bayan bayyana Shugaban Kasa Muhammadu Buhari amatsayin wanda ya lashe zaben da akayi ranar Assabar 23rd Feb 2019 karo na biyu.
2. Kwatsan Babban mataimaki Na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jahar Kebbi H.E Sanata Abubakar Atiku Bagudu Matawallen Gwandu Sarkin Noman Najeriya Alh Faruku Musa Yaro Enabo P.A Wamban Suru, KHADIMATUDDEN Dan MALIKIN Sakaba ya kira Dubban Matasa Magoya bayan Jamiyar Apc don Jagorantar Matasa Maza da Mata da dattijawa domin bayyana ma duniya Farin cikin Alummar Jahar Kebbi bisa wannan Nasara da Jam'iyar Apc tasamu.
3. Maigirma P.A na tareda tawagar Manya manyan Matasa "yan siyasa dake Jahar Kebbi dasuka Hada da Shugaban Kungiyar Buhari Bagudu Support Organisation BBSO na Jahar Kebbi Hon Umar Altine Suru Danfari kuma Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar mulki ta Suru kana Dan Takarar Dan Majalisar Dokokin Jahar Kebbi mai Wakiktar Karamar Hukumar mulki ta Suru.
4. Daga Cikin Tawagar akwai Shugaban Majalisar Shugabannin Jamiyar Apc na Kananan Hukumomin Jahar Kebbi 21 Alh Abdullahi Usman Andare ( APC ALGON KEBBI STATE ) sai Alh Abdulkarim Ad Cashier na Gidan Gwannatin Jahar Kebbi, Engr Aminu Kura na ma'aikatar Ruwa da wutar Lantarki na Jahar Kebbi, Alh Misbahu Maimai Dan Kwangila, Alh Haruna Ladan.
5. Sauran sun hada da Mataimakin Shugaban Karamar Hukumar mulki ta Birnin Kebbi Hon Usman Rima, sai mai baiwa Gwamnan Jahar Kebbi Shawara kan harkokin wasanni Alh Rilwanu Auwal Chief Supporter, Alh Usman Osho, Hon Nura Muhammad Gayya, Hon Hussain Yauri 'Yan fanco, da sauran Masoya maza da Mata dake Fadar Maigirma P.A.
6. Tawagar dai ta tashi ne daga Fadar Maigirma P.A dake Gidan sa inda ta zarce Shiyar Baiti dake Cikin Tudun wada Birnin Kebbi, Sai Shiyar takalau, daga nan tawagar tagarzaya Shiyar "Yar Yara zuwa Kofar Kola acikin Babban Birnin Jaha.
7. Tawagar ta yada zango a Illelar Yari zuwa Makerar Gandu, daga nan tazarce Shiyar Badariya inda tadawo Rafin Atiku daga nan ne tawagar Karkashin Jagorancin Maigirma P.A ta garzaya Titin Ahmadu Bello zuwa Shatale talen Sarki Yahaya dake Birnin Kebbi.
8. Tawagar ta kara zarcewa zuwa Titin Masarautar Abdullahin Gwandu inda ta shiga Shiyar Go slow ta karya zuwa Titin Gidan man Zanzo Kangiwa na Dr Hussaini Sulaiman Kangiwa har zuwa Titin Filin idi zuwa Ofishin Jamiyar Apc na Jahar Kebbi.
9. Tawagar dai har wayau bata tsaya anan tareda dukkan yan tawagar dasuka hada da Yan Kabu Kabu masu agwagwa da Buje zuwa Titin Shatale tale na Rima zuwa Garin Gwadangwaji inda Tawagar ta shiga Garin Gwadangwaji da kuma unguwar Gwannati ta Gwadangwaji.
10. Daga nan ne tawagar takama hanyar dawowa Masauki inda tabiyo tagidan Gwannatin Jahar Kebbi zuwa masauki a Fadar Jagoran Tafiyar Alh Faruku Musa Yaro Enabo.
11. Da yake bayyana farin cikin sa Maigirma P.A Alh Faruku Musa Yaro Enabo yayi Godiya ga Allah bisa wannan Ni'imar da yayima "Yan Najeriya nasake basu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari amatsayin sabon angon Najeriya da Sanatotin Jahar Kebbi Guda Ukku da "Yan majalisun Tarayya Guda takwas duk a Jamiyar Apc Sak. Yaqara dacewa aiki daya yarage ma Alummar Jahar Kebbi shine sake fitowa ranar Assabar 9TH Maris 2019 domin Sake Zaben Maigirma Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu Matawallen Gwandu Sarkin Noman Najeriya da "yan majalisun sa Guda 24 don cigaba da raya karkara da biranen Jahar Kebbi.
12. Shima da yake Jawabi Hon Umar Altine Suru Danfari yayi kira ga Matasan Jahar Kebbi dasu sanya hankuri juriya da hikima wajen tabbatar da ingantacciyar siyasa domin cigaban Al'ummar Jahar Kebbi da kasa Baki daya.
13. Anashi Bangare Alh Abdullahi Usman Andare yayi ma Alummar da suka bada lokacin su wajen yin wannan Zagayen fatar Alkhairi da kuma Godiya har wadanda basu samu damar zuwa ba amma sun bayyana Farin cikin su bisa dandazon Al'umma da suka gani ta Yanar Gizo watau Social Media.
Buhari Bagudu New Media Reporters
Daga Fadar Maigirma Jagora
Alh Faruku Musa Yaro Enabo
(Wamban Suru, KHADIMATUDDEN)
Alhamis 28th February 2019.
Comments
Post a Comment