KWANA DARI (100): GIDAUNIYAR NANAS SUN TAIMAKAWA MATA MARASA LAFIYA A ASIBITOCIN BIRNIN KEBBI DA KALGO LGA.
KWANA DARI (100): GIDAUNIYAR NANAS SUN TAIMAKAWA MATA MARASA LAFIYA A ASIBITOCIN BIRNIN KEBBI DA KALGO LGA.
Daga cikin ayyukan da mai girma Matar Gwamnan jahar Kebbi, Hajiya Nafisa Nasir Idris Kauran Gwandu tayi domin murnar cikarsu kwana 100 akan mulki, Hajiya Nafisa Nasir Idris ta raba kayan abinci, kudi da sauran kayayyaki ga Mata marasa lafiya dake a asibitocin Birnin Kebbi da Kalgo a Jahar Kebbi.
A yayin ziyarar gani da ido da tayi jiya inda ta fara daga Vesico Vaginal Fistula (VVF) Center, mai girma Matar Gwamnan jahar Kebbi kuma wadda ta assasa gidauniyar Nafisa Nasir Charity Development Foundation (NANAS) tace, makasudin ziyarar da tayi shine domin tallafawa marasa lafiya domin rage musu radadi. Ta yaba wa ma’aikatan kiwon lafiya da kokarin da suke yi na kula da marasa lafiya.
A nasu jawabin, Sakatare na din din din na ma’aikatar kiwon lafiya, Dr Nuhu Koko, Dr Hassan Warah, likitan fida ta VVF, Dr Amina sunyi godiya ga mai girma Matar Gwamnan jahar Kebbi da ta kai musu ziyara kuma ta tallafawa marasa lafiya, suka yi mata addu’ar Allah ya saka mata da alkhairi.
Sun kara da yima mai girma Matar Gwamnan jahar Kebbi bayanin nasarori da kuma kalubalen da suke samu a asibiti, suka kara da cewa, asibitin suna koyawa marasa lafiya sanao’in hannu kuma suna basu kayan fara sana’ar bayan sun samu lafiya domin su dogara da kansu.
Mai girma Matar Gwamnan Jahar Kebbi ta zagaya asibitocin domin ta hadu da marasa lafiya masu jiran aiki da wayanda aka yima aikin ta raba musu abinci, yayan itace, turamen zane, dettol da kuma kudi.
Mai girma Matar Gwamnan jahar Kebbi tayi hakan a duka asibitocin Fati Lami, Sir Yahaya, Federal Medical Center, Kebbi Medical Center Kalgo, asibitin Amanawa dake Kalgo. Tayi tattaunawar sirri da shuwagabannin asibitocin, Dr Abubakar Zaki dake Sir Yahaya, Dr Nura Kangiwa dake Medical Center Kalgo, Shugaban Federal Medical Center da kuma Alhaji Muhammad Umar Amanawa.
Matar mai Girma Jahar Kebbi tayi alkawarin bayar da kekunan dinki ga matan da aka horassuwa a VVF kuma ta dauki nauyin yin aikin marasa lafiya arba’in da biyu (42) a asibitocin da ta kai ziyara kuma ta raba kayan haifuwar da suka kai naira miliyan biyu da rabi (2.5 million) a asibitin FMC dake Birnin Kebbi.
Daga cikin wayanda suka yima matar mai girma Gwamnan jahar Kebbi rakiya sun hada da matar mataimakin Gwamnan Jahar Kebbi, matar Sakataren Gwamnati da matar Shugaban ma’aikatan Jahar Kebbi. Sauran sun hada da Matan Kwamishinoni da kuma Kwamishina ta ma’aikatar dake kula da walwala da jindadin mata ta jahar Kebbi.
Ibrahim Mahe
SSA New Media office of Her Excellency, Hajiya Nafisa Nasir Idris Kauran Gwandu
Comments
Post a Comment